May 21, 2024

SHUGABAN KASA TINUBU YA JAJANTAWA IRAN AKAN RASUWAR SHUGABAN KASA RAISI

.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa rasuwar shugaba Ebrahim Raisi; Ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian, da wasu jami’ai a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

Shugaba Tinubu ya bayyana matukar bakin cikinsa kan wannan bala’i mai tada hankali tare da bayyana shugaba Raisi a matsayin jagora mai kishin ci gaban Iran.

Yayin da yake jajantawa iyalan wadanda suka rasu, shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya karawa al’ummar Iran zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba.

A madadin gwamnati da al’ummar Najeriya, shugaban ya tabbatar wa Jamhuriyar Musulunci ta Najeriya goyon baya da addu’a a wannan lokaci na bakin ciki.

Chief Ajuri Ngelale
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman
(Media & Jama’a)

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “SHUGABAN KASA TINUBU YA JAJANTAWA IRAN AKAN RASUWAR SHUGABAN KASA RAISI”