Shugaban Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ya Bukaci A Dakatar Da Yiwa Shari’ar Kasar Gyara.

Shugaban haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) Isaac Herzog yayi kira ga firai ministan kasar Benjamin Natanyahu ya dakatar da shirinsa na yiwa tsarin shari’ar kasar garambawul.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto tasha ta 2 ta HKI tana fadar haka a safiyar yau Litinin. Herzog ya kara da cewa yanzu ba batun siyasa ake yi ba, ana batun Baraka ta shiga har cikin sojojin kasar, sannan duniya gaba daya ta sanya ido tana kallon abinda ke faruwa a haramtacciyar kasar.
Labarin ya kara da cewa an gudanar da gagarumin zanga-zangar kin jinin shirin Natanyahu na yiwa tsarin shari’ar kasar ne bayan da ya kori ministan yakin kasar Yoav Gallant wanda yayi masa nasiha kan ya dakatar da shirin nasa na gabatar da sauye sauye a tsarin shari’ar kasar.
Sai dai wasu majoyoyin gwamnatin Natanyahu sun bada sanarwan cewa zai bayyana dakatar da cikin nasa a safiyar yau litinin, amma kuma daga baya ya fasa. Wannan ya nuna cewa akwai wasu matso tsatsauran ra’ayi tare da shi wadanda suke hana shi dawowa daga shirin nasa duk tare da barakan da aka samu a cikin mutanen kasar, wanda kuma ya kai ga jami’an sojojin kasar