March 1, 2024

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan sojojin mamaya na Isra’ila

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan sojojin mamaya na Isra’ila kan harbe-harbe kan daruruwan Falasdinawa da ke jiran agajin abinci, a daidai lokacin da ake fama da yunwa da ba a taba gani ba a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.

Yayin da yake nuna matukar bacin rai a al’amuran da suka kunno kai daga Gaza, Macron ya yi kira da “gaskiya, adalci, da mutunta dokokin kasa da kasa,” a cikin wata sanarwa ta X.

Yayin da yake bayyana yanayin Gaza a matsayin “mummuna”, Macron ya bukaci “kare fararen hula” tare da jaddada bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa don saukaka rarraba kayan agaji

Acewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, akalla Falasdinawa 104 ne suka mutu yayin da wasu fiye da 760 suka samu raunuka a harin da IOF ta yi a kan titin al-Rasheed a ranar Alhamis.

© Al-mayadeen

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan sojojin mamaya na Isra’ila”