Shugaban Cheheniya Zai Bada Kudi Ga Wanda Ya Kamo Sojojin Ukiraniya Da Su Ka Wulakanta Alkur’ani Mai Girma

Shugaban Jamhuriyar Checheniya ya sanya kudin da su ka kai Robul miliyan 5 ga duk wanda ya kashe wani sojan kasar Ukiraniya da ya wulakanta alkur’ani mai girma, wanda kuma ya kamo shi a raye za a ba shi Robul miliyan 10.
Shugaban na jamhuriyar Checheniya Ramadan Kadirov ya rubuta a shafinsa na “ Teligram” cewa; Ba zan bata lokaci wajen yin tir da aikin ashararun mutane ba da su ka kona al’kur’ani mai girma. Kun riga kun ga bidiyon abinda ya faru a shafina. Domin kawo karshen wannan irin kazaman mutanen na sanya ladar Robul miliyan 5 da duk wanda ya yi maganinsu, wanda kuma ya kawo su a raye, yana da linkin hakan da shi ne Robul miliyan 10. Kuma wannan ladar da na sanya tana nan a ajiye ga duk wanda ya aiwatar da hakan daga nan zuwa kowane lokaci ne a gaba.”
Shugaba Kadrov ya aika da sako zuwa sojojin na Ukiraniya da su ka ci zarafin alkur’ani suna cewa: Ku sani cewa sakamakon abinda ku ka aikata zai same ku a kowane loakci kuma a duk inda kuke a boye. Daga yanzu kun yi hannun riga da zaman lafiya, matsorata kawai.”