July 28, 2021

SHUGABAN AMURKA JOE BIDEN, YA BAYYANA CEWA, SOJOJIN KASARSA ZA SU KAWO KARSHEN AIKINSU NA YAKI A IRAKI ZUWA KARSHEN WANNAN SHEKARA

SHUGABAN AMURKA JOE BIDEN, YA BAYYANA CEWA, SOJOJIN KASARSA ZA SU KAWO KARSHEN AIKINSU NA YAKI A IRAKI ZUWA KARSHEN WANNAN SHEKARA.

Joe Biden ya bayyana haka ne a jiya, yayin da yake ganawa da Firaministan Irakin Mustafa al-Kadhimi dake ziyara a Amurkar.

Shugaban ya ce aikinsu a Iraki shi ne ci gaba da bayar da horo da taimako, da taimakawa wajen tunkarar kungiyar IS idan akwai bukata, amma zuwa karshen bana, Amurka ba za ta shiga yake-yake ba.

Yanzu haka akwai kimanin dakarun Amurka 2500 a kasar Iraki.

An tura dakarun kawance da Amurka ke jagoranta zuwa Iraki ne, domin taimakawa dakarun kasar a yaki da kungiyar IS da horar da su tare da ba su shawara.

A Iraki dai akwai bangarorin al’umma da dama dake bukatar ficewar sojojin Amurka daga

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “SHUGABAN AMURKA JOE BIDEN, YA BAYYANA CEWA, SOJOJIN KASARSA ZA SU KAWO KARSHEN AIKINSU NA YAKI A IRAKI ZUWA KARSHEN WANNAN SHEKARA”