Shugaba Tinubu Ya Sake Nada Sabbin Mukamai

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da nada kakakin majalisar wakilan kasar, Femi Gbajabiamila a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne bayan gana wa da gwamnonin jam’iyyarsa ta APC a fadar shugaban kasar a Abuja ranar Juma’a.
Haka kuma shugaban kasar ya nada Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Jigawa, a matsayin mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar.
Kazalika Tinubu ya nada George Akume, tsohon gwamnan Jihar Binuwai kuma Ministan Ayyuka na Musamman a gwamnatin tsohon shugaban kasar Buhari, a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Wadannan nade-nade su ne na farko da Shugaba Tinubu ya yi tun bayan shan rantsuwar kama mulki a ranar Litinin 29 ga wayan Mayun da ya gabata.
Taron gwamnonin APC din da Shugaba Tinubu ya samu halartar gwamnonin jihohin Legas Babajide Sanwo-Olu da Nasarawa Abdullahi Sule da na Jigawa Umar Namadi da na Gombe Inuwa Yahaya da na Kogi, Yahaya Bello da na Borno Babagana Zulum da kuma na Yobe Mai Mala Buni.
Sannan akwai gwamnonin jihohin Kaduna Uba Sani da Dikko Radda na Katsina da Father Hyacinth Alia Binuwai da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara da Dapo Abiodun na Ogun da Umar Bago na Neja da Aliyu Ahmed na Sokoto da Francis Nwifuru na Ebonyi da kuma Bassey Otu na Cross River.