September 18, 2021

Shugaba Buhari Zai Halarci Taron Majalisar Dinkin Duniya A New York

Daga Balarabe Idriss


Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa birnin New York na kasar Amurka a gobe Lahadi don halartar taron majalisar dinkin duniya.

Shugaban zai halarci taron majalisar na zango na 76 wanda aka kira da (UNGA76).

Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Femi Adesina a bayanin da ya wallafa ya bayyana cewa shugaban zai samu rakiyar Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama; Antoni janar Ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN); Karamin Ministan muhalli, Sharon Ikeazor.

 

Ya kuma kara da cewa wakilan shugaban sun hada da Mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasa Mejo Janar Babagana Manguno (mai ritaya); Ambasada Ahmed Rufai Abubakar, Abike Dabiri-Erewa da sauran su.

 

Ya kuma kara da cewa tattaunawar bana a wurin taron zai ta’allaka ne akan sake farfadowa daga annobar Korona, sake gina al’umma da kuma amsa bukatun duniya kana kuma da girmama hakkokin al’umma.

Daga karshe ya bayyana cewa ana sa ran dawowar shugaban da tawagar sa zuwa Najeriya a ranar Lahadi 26 ga watan Satumba.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Shugaba Buhari Zai Halarci Taron Majalisar Dinkin Duniya A New York”