January 14, 2024

Shin zai yiwu Allah ya jarabci mutum tun kafin ya halicce shi?

1 – Shin zai yiwu Allah ya jarabci mutum tun kafin ya halicce shi? Ko an kallafa musu wani abu kafin halitta?
2 – Wace irin jarrabawa Allah ya yi sayyida Fatima (a.s)? Ya lamarin ya kasance?

Amsa:
Abin da ake nufi da jarrabawa da dangoginta shi ne:
A yaren Larabci, idan aka ce: Jarrabawa, ana nufin: Gwaji ko neman qarin bayni. Idan aka ce da kai: Ka gwada mutum kafin ka yi abota da shi, ko kafin ka yi mu’amala da shi. Ana umartar ka ne da neman qarin bayani, ko kuma sanin halin da mutum yake ciki, don ka san haqiqanin halin da yake ciki. Da haka ne kuma za ka tabbatar da gaskiyar wanda ya ba ka labari game da shi, ko ya kawo maka shi domin ku yi wata hulxa da shi.
Jarrabawa tana da nau’o’i da dama, kuma ta bambanta da dalilin da ya sa za a yi ta. Kuma tana bambanta da bambancin mai jarrabawar da kuma wanda za a jarraba.
Jarrabawa tana iya kasancewa: Ta hanyar tambayar wanda za a gwada, kamar yadda malami yake tambayar xalibansa. Da haka ne zai san irin yadda suka fahimci darasin nasa, da irin yadda suka shirya wa tambayoyin nasa.
A wani lokacin kuma, tambayar tana kasance wa ga macen da mutum yake son ya aura, don ya fahimci irin yadda ta fahimci rayuwar aure, da wayawar da take da ita game da zamantakewa, kafin ya bijiro mata da bukatarsa na son ya aure ta. Haka ita ma za ta iya yin tambayoyi ga namijin da take so ta aura, don ta fahimci wasu daga cikin halayyarsa, mai fushi ne ko mai saurin hannu ne, ko irin wanda idan aka yi masa kuskure yana da saurin hannun kai duka, mai kyauta ne ko marowaci?!
A wani lokacin kuma gwajin ko jarrabawar tana kasancewa ne ga bukatar sanin irinn gogewar da mutum yake da ita. Kamar ka shiga harkar kasuwanci ‘yar qwarya-qwarya, keventacciya, ga wanda kake son saka shi a cikin dukiyarka, don ka tabbatar da gaskiyarsa da riqon amanarsa, kafin ka tsunduma shi a cikin kunzumin dukiyarka mai faxi.
A wani lokacin kuma ana gwada mutum ne, don sanin irin matakin da yake iya xauka, idan ya shiga matsala ko wata damuwa, ko takura. Sai ka gwada shi ta hanyar tsokanarsa, domin ka ga irin juriyar da yake da ita, da irin yadda yake iya mallakar kansa a yayin da ya tsinci kansa a cikin matsi ko takura, ko idan aka fusata shi. Da haka ne za ka fahimci cewa: Shi mai haquri ne ko mai raki? Shin mai hankali ne shi ko kuwa wawa ne?!
Irin waxanda duk zaman lafiyar da suke da kake yi da su, idan ka fusata su, sai su rufe ido su keta ka, ya numa maka cewa: Shi fa da ma can ba shi da mutunci, ko kuma shi fa tsohon xan iska ne…

 

© Tare da Sheikh Mujtaba Adam kano.

SHARE:
Makala 0 Replies to “Shin zai yiwu Allah ya jarabci mutum tun kafin ya halicce shi?”