August 24, 2021

Shigar ‘yan bindga makarantar “NDA”: Jama’a sun nuna tashin hankalin su

Daga Muhammad Bakir Muhammad

Kamar yadda rahotanni suke zuwa mana, a talatainin daren ranar talata ne yan bindiga suka fada bakirin “Afaka” na makarantar horon sojin Najeriya (NDA) Kaduna a yayin da suka harbe wani Laftanar daga cikin sojin gidan mai suna Wulah tare da wani babba mai suna CM Okoronwo wanda hakan yayi sanadin rasa rayukan su, sannan daga bangare guda kuma wasu daga cikin sojojin an yi awun gaba da su.

Tuni dai mutane suka yi ta tofa albarkacin bakin su kan lamarin, a yayin da wasu ke ganin hakan a matsayin gazawar bangarorin tsaro na Najeriya.

Wasu kuwa sun nuna cewa yanzu ta tabbata babu wanda yake da tabbataccen tsaro a kasar, don haka rayuwar kowa na cikin barazana.

A yayin da jaridar Daily Trust ta fidda rahoton, mutane sun yi ca wurin fadin ra’ayoyin su, a sadda wasu ke nuna “…in har makarantar hoton soji zai zama haka to babu makawa addua kadai zai kwace mu a kasar nan”

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Shigar ‘yan bindga makarantar “NDA”: Jama’a sun nuna tashin hankalin su”