August 4, 2021

SHEIKHUL DUSI (Qs)

Shine Muhammad dan Hassan dan Ali dan Hassan Addusi, Wanda akafi sani da SHEIKHUD-DA’IFA.

An haife shi garin Dus, cikin kasar a yanxu, watan Ramadan shekara ta 385 BH (bayan Hijra).

A shekarar 408AH, ya tafi Baghdad (Markazin Ilmi a wancan lokacin), sannan Babban Birnin Khalifanci a lokacin. Yayi Karatun a wajan Malamai manya a baghdad, daga nan ya kasance tare da Babban Malamin Nan SHEIKHUL MUFID (Qs),  na tsawon Shekara biyar, bayan rasuwar Sheikul mufid, sai Sheikul Dusi ya zama cikin manyan Daliban Sayyed Murtadha Alamul Hudha har rasuwarsa.
Bayan rasuwar Sayyed Murtadha Alamul Hudha a shekara ta 436BH, sai Sheikul Dusi ya zama jagoran Shi’a daga Wannan lokacin Inda ya jure wahalhalu da dukkan nayin Jagoranci.
Ya zauna a Baghdad har zuwa shekara ta 448AH, har zuwa lokacin da sabani ya faru babba tsakanin Musulmi, sai Sheikul Dusi ya bar Baghdad zuwa Najaf.
Daga Wannan lokacin ne Najaf ta zama wajan taruwar daliban Addini, suka cigaba da karatu a kusa da kabarin Imam Ali (a.s).
A Shekara ta 460BH, Sheikul Dusi ya rasu a gidansa wanda aka maida shi Masallaci, kamar yadda ya bukata a wasiyarsa, wanda a yanxu ake kiransa da

MALLACIN SHEIKUL DUSI.
Daga Littafansa: Ya bar littafan daya rubuta sama da 50, a fannoni da dama na ilmi, daga ciki akwai TAHZIBUL AHKAM, AL’ISTIBSAM…., RIJALU SHEIKUD DUSI, ATTIBYANU FI TAFSIRUL QUR’AN  dadai sauransu.
Allah yai masa rahama…

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “SHEIKHUL DUSI (Qs)”