December 16, 2023

Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Jaber Al Sabah shugaban kasar Kuwait ya rasu yana da shekaru 86 a duniya a yau Asabar

Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Jaber Al Sabah shugaban kasar Kuwait ya rasu yana da shekaru 86 a duniya a yau Asabar.

A karshen watan Nuwamba ne aka kwantar da Sarki Nawaf a asibiti sakamakon matsalar rashin lafiya. Ana sa ran wanda zai gaje shi zai kasance dan uwansa, Yarima mai jiran gado Sheikh Meshal al-Ahmad al-Jaber Al Sabah, mai shekaru 83 a duniya.

Nawaf ya hau karagar mulki ne a shekarar 2020 bayan rasuwar dan uwansa Sheikh Sabah al-Ahmad al-Jaber Al Sabah.

An haife shi a shekara ta 1937, Sheikh Nawaf shine ɗa na biyar ga Sheikh Ahmad al-Jaber Al Sabah, shugaban Kuwait na 10, wanda ya jagoranci ƙasar kusan shekaru talatin a farkon karni na 20.

Nawaf ya fara tafiyarsa ta siyasa tun yana da shekara 25 a matsayin gwamnan lardin Hawalli sannan ya rike mukamai daban-daban a gwamnati.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Jaber Al Sabah shugaban kasar Kuwait ya rasu yana da shekaru 86 a duniya a yau Asabar”