December 10, 2023

Shehu Nuru Maulana.

Amjad Mukhtar Imam 

A duk inda kaga ɗan Adam zaka same yana sa’ayi ne zuwa ga kamala, idan kaga kirista zaka same shi i’itiqadin shine ya kaiga ga bautan abinda yake bautawa, haka musulmi (Sunnah da shi’a).

 

Amma zaka samu mutum yakan riƙi wani wasila domin isa zuwa ga wannan kamala, bayan ya riƙi Allah da Manzo (S) ya riƙi Ahlulbaiti (AS) zuwa kan Imam Mahdi (Atfs) sai Maraji’ na addini waɗanda Imamul-Hujjah yayi mana ishara da komawa garesu domin ɗaukan masa’il na addinin mu.

 

Sai na duba da kyau naga wannan waliyyin Allah Sheikh Nur Dass (H) ya zama min wani samfuri kuma abin koyi a janibin “Akhlaq, Zuhudu, Wayewa, Ikhlasi, Yawan Ibada, Da fatan Alkairi ga dukkan mutane…

 

Idan muka ɗauki janibin Akhlaq na samu Sheikh Nur (H) mutum ne mai kyawawan ɗabi’u, da iya mu’amala ta yadda duk nisan dare ka kira wayar shi zai ɗauka kuma ya saurare ka, yakan bawa mutum shawara tare da shajja’a shi kan neman halal da neman ilimi…

 

Idan ka ɗauki janibin zuhudu zan iya ce maka wallahi Sheikh Nur (H) waliyyin Allah ne, domin muddin ka kasance mai tsarkin ruhu zaka iya gane cewa yana nan kan السير والسلوك saboda babu ranar da zai ce maka ni wanene, watarana anyi zaman ƴan media a Husainiyyar Rasulul A’azam kowa yana faɗin sunan shi, da aka zo kanshi sai yace: Sunana Muhammad Nur, take naji idanuna sun ciko da hawaye, sam duniya da abinda ke cikin ta basu tsole masa ido ba, bare su zamto sune bukatar shi…

 

Mutum ne wayayye da yake son yaga duk wani ɗan shi’a ya waye, kama daga sanin addini da sanin lammuran da suka shafi yau da kullum.

 

Sheikh Nur Dass (H) ya hidimawa ƴan shi’a ta kowane ɓangare, domin dawowar shine ya samar da Hauzozin Shi’a da masallatan a garuruwan Kano, Kaduna, Katsina, Gombe, Bauchi, Azare, Yobe da sauransu, wannan aike ne da kafin shi ba’a samu hakan ba, na tabbata wannan zai farantawa dukkanin mabiya Ahlulbaiti na ciki da wajen Nigeria.

 

Haɗuwata dashi kuwa ya kasance kamar haka: “Mun tura sakon tambaya ne ofishin Ƙa’id (DZ) sai aka ce mu tuntuɓi Abu Sadiq a nan Nigeria domin shine wakilin Shari’a” Daga ranar da na fara tuntubar shi zuwa yau na fa’idantu sosai, sannan a sanadin shi naje daurori da karatu, har nasan Aƙidata zuwa yau.

 

Ina roƙon Allah ya kare shi, ya ƙara masa lafiya da nisan kwana cikin hidimtawa Ahlulbaiti (AS).

SHARE:
Makala 0 Replies to “Shehu Nuru Maulana.”