July 28, 2021

SHEDAN BAI DA IKO KO TASIRI AKAN BAYIN ALLAH NA GARI BALLANTANA ANNABAWA KO MANZANNI MUSAMMAN MA ANNABI MUHAMMAD (SAWA).

SHEDAN BAI DA IKO KO TASIRI AKAN BAYIN ALLAH NA GARI BALLANTANA ANNABAWA KO MANZANNI MUSAMMAN MA ANNABI MUHAMMAD (SAWA).

 

Dangane da fadin Allah Ta’ala cewa “Alam nashrah laka sadrak”

“Shin ba mu yalwata maka zuciyarka ba”?

 

Akwai wasu ruwayoyi wanda suka zo cikin littafan hadisai da na tarihi wanda su ke nuna cewa yana daga hanyar da aka yalwata zuciyar Annabi (sawa) tsaga zuciyarsa da aka ce Mala’iku wai sunyi, kana suka cire rabon shedan daga wannan zuciya mai albarka ta Ma’aiki (sawa) kamar yadda ya zo a tarihin Ibnu Hisham da Muslim a cikin littafinsa na hadisi.

Wadannan ruwayoyi da suke nuna an cire rabon shedan daga zuciyar Manzon Allah (sawa) da wadanda ke nuna cewa dukkan dan Adam (hatta Ma’aiki) wai shedan ya soke shi a jikinsa lokacin da za a haifeshi face Isa bin Maryam da Mahaifiyarsa su shedan bai soke su ba, kamar yadda ya zo a Buhari.

Malamai masu bincike da bin diddigi sun tabbatar da rauni da rashin asalin wadannan hadisan a cikin ruwayoyin musulunci ingantattu. Zance mafi tabbata shi ne cewa wadannan ruwayoyi ne wadanda aka samo daga Yahudawa. Yana daga abinda ake nuna rashin ingancinsu, in an dubi ruwayoyin da kyau, menene zai sa a ce:

 

1- “Dukkan dan Adam shedan ya soke shi “hatta Ma’aiki” amma sai aka ke6e Annabi Isa (as) da mahaifiyarsa aka ce su shedan bai soke su ba ?

 

2- Shin me ake so a nuna a wannan ruwayar ? Ashe ba so ake a tabbatar da akidar kiristoci ba na cewa Isa (as) dan Allah ne ko abinda yayi kama da haka

na nuna fifikonsa akan dukkan talikai ? Alhali kuwa dukkan addinan Allah sun yi ishara kan cewa Manzon Allah Annabi Muhammadu (sawa) shi ne fiyayyen talikai.

 

3- Kana menene zai sa a ke6anci Manzo (sawa) da wannan tsaga zuciya (tiyata) alhali dukkan Annabawa ba a ruwaito an yi musu haka ba ?

 

4- Kuma a wani dalili ne za a ce har Ubangiji Madaukaki Ya azabtar da ManzonSa da irin wannan nau’i na azaba?

 

5- Ashe Ubangiji ba zai iya halittar Ma’aiki tun farko da zuciya tsarkakakka ba, ba tare da Ya bukaci aiko Mala’iku domin su zo su tsaga zuciyarsa ba ?

 

Shin hakan bai sa6a wa irin ayoyin da suka zo a cikin Alkur’ani Mai girma ba?

Wadanda suke nuna cewa shedan bai da wani iko ko dama a kan bayin Allah na gari.Kamar yadda shi (shedan) din da kansa ya yi ikirari da hakan, wurin da ya zo a cikin Alkur’ani: ya ce: “Ya Ubangina a sanadiyyar 6atar da ni da ka yi (saboda sa6a maka da na yi) to lallai zan kawata musu a bayan kasa, kana tabbas zan 6atar da su gaba dayansu, face tatattun bayinka daga cikinsu. Suratul Hijr aya ta 39-40.

 

Hakanan a cikin Suratul Isra aya ta 65: Allah Yana cewa: “Hakika bayina (kai Iblis) ba ka da wani iko akansu”. kamar kuma yadda ya kara zuwa a cikin Alkur’ani Mai girma a Suratun Nahl aya ta 99 cewa “Hakika shi (Iblis) ba shi da wani iko a kan wadanda suka yi Imani kuma suke dogaro kan Ubangijinsu”.

 

To wadannan ayoyin idan aka dube su da idon basira sai a samu cewa shi shedan bai da wani iko ko tasiri akan bayin Allah na gari ballantana Annabawa, ko Manzanni, musamman ma shugabansu Annabi Muhammad Manzon tsira (sawa)

 

GASKIYAR AL’AMAARI Shi ne; kamar yadda ya zo a littafin Al agani mujalladi na 3 Cewa wannan ruwayar an samo ta ne daga cikin tatsuniyoyin larabawan jahiliyya. Yanda tatsuniyar ta ke shi ne: “Umayya dan Abi salt wata rana yana barci sai wasu tsuntsaye biyu suka zo, sai dayansu ya tsaya a bakin kofa, dayan ya shiga cikin dakin da yake kwance, ko da shigarsa sai ya tsaga kirjinsa ya fito da zuciyarsa kana sai tsuntsun ya mayar wa Umayya da zuciyarsa, sai daya tsuntsun ya tambayi dan uwansa ya ce: shin ya farfado? Sai ya ce: E. Kana tsuntsun ya sake cewa: shin ya tsarkaka? Sai ya ce a’a bai tsarkaka ba”.

 

Wannan tatsuniyar ta zo a, Agani da siga daban – dabam. To tun da ya tabbata cewa wannan tatsuniyar sananniya ce a wajen larabawan jahiliyya, to kokarin dangana ta da aka yi ga Ma’aiki (sawa) ba komai ya ke nunawa ba sai dai neman karfafa wasu gur6atattun akidu, da kuma neman sukan gaskiyar da Alkur’ani ya ke tattare da ita, kana kuma da nuna kokwanto kan ismar Manzo (sawa), wato nuna kokwanto kan irin garkuwa da kuma kariya da ya ke da ita daga Allah na rashin aikata sa6o da samun mashigar shedan tun azal kamar sauran Annabawa da Manzanni, kai fiye ma da su.

 

 

 

Daga:

Mallam Mahmud Maikasida

SHARE:
Makala 0 Replies to “SHEDAN BAI DA IKO KO TASIRI AKAN BAYIN ALLAH NA GARI BALLANTANA ANNABAWA KO MANZANNI MUSAMMAN MA ANNABI MUHAMMAD (SAWA).”