May 24, 2023

Senegal : Sai A Ranar 1 Ga Watan Yuni, Jagoran ‘Yan Adawa Zai San Makomarsa

A daren jiya mai gabatar da kara a kotun Dakar ya bukaci daurin shekaru 10 a gidan yari kan laifin fyade ko kuma daurin shekaru 5 a gidan yari saboda bada cin hancin ga matasa.

Lauyoyin dan adawan dai sun yi tir da abunda suka kira tauye hakkin wadan sukke karewa, inda suka fice daga kotun a msatyin nuna rashin gamsuwa.

jiya Talata ne aka koma gaban kotu don ci gaba da sauraron shari’ar jagoran yan adawar na Senegal Ousmane Sonko kan laifin fyade da ake tuhumarsa da shi, sai dai bai bayyana gaban kotun ba a karo na biyu.

Dan siyasar mai shekara 48, ya ce shari’ar da aka soma a makon da ya gabata, na da alaka da siyasa da kuma yunkurin hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa.

Magoya bayansa dai sun toshe hanyar da ta dangana da gidansa domin dakatar da yunkurin kama shi a gidansa dake yankin Ziginchor.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Senegal : Sai A Ranar 1 Ga Watan Yuni, Jagoran ‘Yan Adawa Zai San Makomarsa”