Senegal : An Yankewa Madugun ‘Yan Adawa Hukuncin Daurin Shekaru Biyu

Kotun hukunta manyan laifuka a birnin Dakar Senegal ta yanke wa madugun ‘yan adawa na kasar Usman Sonko, hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari a kan laifin bata tarbiyyar matasa, Sai dai kuma kotun ta wanke shi a kan zargin fyade da ake masa.
Hukuncin daurin dai na nufin Mista Sonko, ba zai iya tsayawa takarar shugabancin kasar ba a zaben da za a yi nan da watanni tara.
Mista Sonko dai bai halarci zaman shari’ar ba.
Hakan dai ya haifar da zaman dar-dar a wannan kasar dake yammacin Afrika, duba da farin jinin da shi Mista Sonkon yake da shi a kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon bayyanin shugaban kasar Macky Sall, akan ko zai nemi yin tazarce domin neman wa’adin mulki a karo na uku ko kuma a’a.
Madugun ‘yan adawan dai na zargin gwamnatin Senegal da yi masa bi ta da kulin siyasa da zumar hana shi tsayawa takara, zargin da gwamnatin ta musanta.
Ƴan sanda dai sun killace hanyar shiga gidan Ousmane Sonkon, inda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa magoya bayansa da suke sukar shari’ar.