May 16, 2023

Senegal : An Dage Shari’ar Dan Adawa Zuwa 23 Ga Wata

 

Kotun birnin Dakar a Senegal, ta sanar da dage shari’ar dan adawan nan Ousmane Sonko har zuwa ranar 23 ga watan Mayun nan.

A ranar Litinin din makon jiya ne kotun daukaka kara ta tsawaita wa’adin wata biyu da aka yanke masa a gidan yari zuwa wata shida, sakamakon bata sunan ministan yawon bude ido na kasar.

Yau Talata ne kuma aka tsara zai fuskanci wata shari’ar da ake yi masa kan zargin aikata fyade da barazanar kisa da wata ma’aikaciyar wani gidan gyaran gashi ta shigar kan shi.

Zarge-zargen da Mista Sonko ya musanta, yana mi cewa bi-ta-da-kullin siyasa ce kawai.

Rahotannid aga Senegal din sun ce akalla mutum ukiu suka rasa rayukansu a zanga zangar data barke a yankin Ziguinchor, ranar Litini a jajibirin gurfanar da shi a gaban kotu, inda magoya bayansa sukayi artabu da jami’an tsaro.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Senegal : An Dage Shari’ar Dan Adawa Zuwa 23 Ga Wata”