December 28, 2022

Sayyidah Fátima (as) tabarwa duniya darussa a fannin thaqafa da siyasa,

Sayyidah Fatima (as) itace mace ta farko a tarihin musulunci wadda ta fito gaba da gaba ta qalubalanci tsarin siyasa da ake shugabantar Al,umma a qarqashinsa a zamaninta,

Me ake nufi da qalubalantar tsarin siyasa a Nan ?

Ana nufin ADawa DA tsarin wani shugabanci da kuma kokarin tabbatar da wani tsarin a madadinsa ,

Fátima (as) ta tsaya tsayin daka ta kare wasiccin Annabi (sawa) kan Imam Ali (as) A matsayin sa na imami kuma khalifa Shar,antacce wanda Allah da Manzonsa suka Ayyana qarara da Nassosi,

Sayyidah Fátima (as) TA tsaya gaba da gaba ta nemi Gadonta da mahaifinta ya barmata na fadak ,a wurin khalifa, kuma ta ja daga da hujjoji daga ALQURANI a gaban shugaban gwamnati a wannan lokaci, a Kan haqqinta,

Dama ance :

لا يعاتب المرء في طلب حقه وانما يعاتب في طلب ما ليس له.

Wato Baa ganin laifin mutum Kan neman haqqinsa kawai ana zarginsa ne wajen neman Abinda ba nasa ba ne ,

Fatima (as) maasumiyace da Ayatut Tahir da ayatul mubahala da suratu Hal,ata, babu mai jayayya kan Haka sai nasibi laananne,

Ke Nan ba zata taba neman Abinda ba hakkinta bane,

Don haka tayi khutba mashahuriya a Madina Mai ratsa zuciya Mai cike da ilimi da sanin dokoin Allah SWT, A gaban SAHABBAI masu tarin YAWA,

Inda ta kasance mace musulma ta farko DA ta tsaya tai wa maza khutba a masallaci a tarihin musulunci,

Muduba khutbarta da Hadisanta da ta kawo ga matan muhajiruna da Ansar tana qalubalantar yadda aka tozarta ta ita da mijinta da yayanta bayan wafatin Annabi (SAWA) ,

Anan zamu fahimci cewa lallai Sayyida Fatima (as) tana da wayewa sosai Kan yadda jagorancin Al,umma ya kamata ya kasance da kuma hadarin da kaucewa tsarin da ALLAH da Manzo ( sawa )suka zaba ma Al,umma yake da hadari ga Addini.

Don haka ta fahimci me take karewa sosai , tana kare Addinin Allah ne da sakon Manzo (SAWA) wanda kare jauharinsa ya tsayu akan samun shugaba Ayyananne zababbe daga Allah da Manzonsa (SAWA),bayan Annabi (sawa)

Shugaba Tsarkakakke DAGA Allah da Manzonsa, masanin sakon Manzo CIKI da waje , ba jahili ba ,kuma Adali gwarzo ,wanda zai ci gaba da tafiyar da Ayyukan Manzo(SAWA) cikin Al,ummah wajen bayanin Sakon Allah SWT da bawa AQIDA kariya da hada kan Al,umma da hanasu RIDDA,

Shi yasa zamu ga a lokacin da ta tunkari khalifa ta nemi ya bata Gadonta yaki ,

da yakawo hujja da hadisi (Hadisul Ahaad ) ba tai shiru ba, domin ta San wannan ba hadisin babanta bane ,

IDAN da mahaifinta ne (SAWA) ya fade shi da sai tafi kahalifa sannin sa da Abinda yake nufi ,Don kuwa sune Masa na sunna ta haqiqa a gidansu a ke saukarda wahahi ,

Kuma SU aka ce a nemi fassarar Addini a wurinsu ba wasu ba,

Wannan umarni ne na Allah da Manzo kuma duk Wani umarni DAGA kan sahabbai yake Farawa,

Don Haka take ta nuna ja, Kan hadisin ta kuma kawo hujjojin da suka fi kowa ce hujja karfi wato Ayoyin Alqur,ani ,

TO ko anan Sayyida Fatima (as) ta nuna kwarewa wajen kafa hujjah ,don ita An kafa mata hujja da hadisi Hadisul Ahaad wanda ba Wani wanda ya TABA jinsa sai khalifa ,ita kuma ta kawo hujja da Al, Qurani wanda shine yankakken da dalili, da BABU shakka a ingancinsa,

Kuma da takawo , shi khalifa Bai kawo wasu nassosi na ALQURANI ba Don kalubalantar nata,

SAI ya kafe A Kan hadisin sa, (Hadisul Ahaad )

Wannan ya nuna mana yadda Sayyida Fatima )as) take da gwarzontaka da tsayawa akan gaskiya da bata kariya,

Hakanan ko ba komai,ZAMU ga cewa mahimmancin AHLULBAIT AS a cikin SANNAN Alumma musamman Fatima (as) a ce tazo wajen Khalifa ta nemi a bata Gadonta lallai hakan Yana nuna cewa akwai wani yanayi na tozarci da AHLULBAIT (as) suka samu kansu ciki a wannan lokaci,

Hakanan matsayin khalifa Kan batun da Fatima (as) tazo masa dashi da yanayin raddin da tayi masa ,ya nuna cewa akwai wani yanayi na maras dadi da zuriyar Annabi SAWA suke ciki a karkashin waccen gwamnati,

Saboda Haka mata zasu iya daukar darusa masu tarin yawa daga matakan da sayyada Fátima (as) ta dauka a fannin siyasa da daawah zuwa ga Addini ,

Ma,ana ba daidai bane mace tace Bata da raayi ko matsaya a tsarin tafi da mulkin Al,umma ,

kamar Yadda ba daidai bane Shima namiji yace ba ruwansa da siyasa. Ba daidai bane,

Su yan mulkin mallaka da yan koransu kullum kokarinsu shine su nesanta maza da mata daga harkar siyasa da gudanar da mulki , tayadda siyasa zata kebanta ne da wasu kebantattun mutane gurbatattu , Alumma kuma tayi ta zama cikin wahala da rudani.

Kamar Yadda lamarin ya kasance tun farko har izuwa lokacin banu,umayya da akaji ma shugaban su yana tabbatar da irin wannan mulkin mallakar na siyasa,

Wato ABU SUFYAN baban MUAWIYYA inda yake cewa :

( تلقفوها يا آل أبي سفيان تلقف الكرة والذي نفس أبي سفيان بيده لا جنة ولا نار ).

أسد الغابة 5 / 216

Wato ; KUYI FASIN DA ITA (WATO KHILAFA ) FASIN IRIN NA BALL ,NA RANTSE DA WANDA RAN ABI SUFYAN YAKE HANNUNSA BABU WATA ALJANNA BABU WATA WUTA )

me wannan magana shine ABU SUFYAN , BABAN MUAWIYYA FARKON WANDA YA YAKI MANZON ALLAH , SHUGABAN TULAQA,U,

wanda ake ce masa SAHABI ya ke rantsuwa babu wuta babu Aljanna, kuma yake dasa tsarin mamaya da mulkin mallaka a tsarin shugabanci,

Don haka su yan mulkin mallaka da yan korensu ba sa son Al,umma su fahimci haqqinsu da yancinsu na siyasa maza ko Mata , basa son kowa ya
Motsa,

Duk da Allah (swt) yana cewa:

وَالْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ يَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَيُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَيُطِيعُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ ۚ أُولَٰئِكَ سَيَرْحَمُهُمُ اللَّهُ ۗ إِنَّ اللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ )

سورة التوبة 71

Wato :

KUMA MUMINAI MAZA DA MUMINAI MATA SASHINSU MAJIBINTA SASHI NE SUNA UMARNI DA KYAKKYAWA SUNA HANI GA MUMMUNA ),

To wannan shine madogarar Sayyida Fatima (as) ,wajen kare gaskiya da tabbatar da adalci da qalubalantar fandara,don a tantance gaskiya da masu ita ,

TA kuma tabbatar da cewa umarni da kyakkyawa da hani da mummuna más,uliyya ce ta namiji da mace ,ba mas,uliyyace ta maza ba kawai.

 

©Sheikh Balarabe yakasai kano.

SHARE:
Makala 0 Replies to “Sayyidah Fátima (as) tabarwa duniya darussa a fannin thaqafa da siyasa,”