November 29, 2022

Sayyida Zainab al-Kubra ‘Yar Imam Ali (a.s)

Tare da Marigayi Sheikh Auwal Bauchi Allah ya lullubeshi da rahma.

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

 

Shakka babu nazari bincike cikin tarihin Ahlulbaiti (a.s) da samun masaniya kan koyarwarsu ta tunani da siyasa lamari ne da ke da muhimmancin gaske wajen fahimtar koyarwa da tafarkin Manzon Allah (sawa) da addinin da ya zo da shi (Musulunci)…don haka ne ma makiya suka ba da lokacinsu ba dare ba rana wajen ganin sun toshe wannan haske da hana al’umma fahimtar irin matsayi da gudummawar da Ahlulbaitin suka bayar wajen ci gaban wannan addini da kuma ‘yantar da al’umma daga duhun zalunci zuwa ga hasken Musulunci. Ahlulbaiti (a.s) dai sun ba da gagarumar gudummawa ta hanyar koyarwarsu, dabi’unsu, jihadinsu na fada da zalunci da kaucewa tafarki da dai sauransu wajen kyautata rayuwar al’umma duniya da lahira.

 

Ko ba a fadi ba waki’ar Karbala mai dacin gaske da ta faru na daga cikin lamurran da suka faru a tarihin Musulunci sannan wanda tafi tasiri wajen ayyana tafarkin Musulunci da kare shi. A wannan waki’a ta Karbala akwai wata madaukakiyar mace daga cikin Ahlulbaitin Manzo (s) da ta ba da gagarumar gudummawa wajen isar da sakon Karbala da kuma ci gaba da kare shi bayan shahadar dan’uwanta Husaini bn Ali (a.s) har zuwa karshen rayuwarta. Wannan madaukakiyar mace kuwa ita ce Zainab al-Kubra ‘yar Aliyu bn Abi Talib da Fatima ‘yar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare su da alayensu). Don haka wannan dan abin da muka rubuta dai zai yi magana ne kan rayuwar wannan baiwar Allah da kuma irin gudummawar da ta bayar, don ta kasance mana abin koyi musamman ma ga matayenmu na wannan zamani, saboda kasantuwansu (Ahlulbaiti) abin koyi gare mu bayan kakansu Ma’aiki mai tsira da aminci, sannan kuma don su kasance mana abin so da kauna saboda fadin kakansu cewa: (ألا و من مات على حبِّ ال محمد مات شهيداً ) “Ku sani duk wanda ya mutu a kan son Zuriyar Muhammadu, ya mutu shahidi”

 

An haifi Sayyida Zainab al-Kubra ne a gidan Ali da Fatima karkashin kulawar gidan Annabci a ranar biyar ga watan Jimada Awwal shekara ta biyar bayan hijira. Babu shakka wannan rana ta haihuwar Zainab ta kasance rana ce ta farin ciki a bangare guda, a bangare guda kuma ta bakin ciki ga juyayi da iyayenta da kakanta Manzo (s). Ranar farin ciki saboda karuwar da Zuriyar Manzo ta samu da kuma irin kariyar da Musulunci ya sake samu, ranar bakin ciki kuma saboda irin abin da zai faru da ita nan gaba daga wajen makiya. Bayan haihuwar Zainab, mahaifiyarta Fatima al-Zahra (a.s) ta dauko ta ta kawo ta wajen mahaifinta Ali (a.s) don ya sanya mata suna…sai dai kamar yadda al’adarsa (Ali) ta ke bai taba wuce Manzon Allah ba wajen dukkan abin da zai gudanar don haka sai ya ce wa Fatima:Lalle ba zan gabaci Manzon Allah wajen sanya mata suna ba, don haka bari mu jira Manzo ya dawo, don a daidai lokacin da aka haifi Zainab, Annabi (s.a.w.a) ya kasance ya yi wata ‘yar karamar tafiya wajen Madina. Don haka lokacin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya dawo, kamar yadda kuma al’adarsa take, idan har ya dawo daga tafiya baya shiga wani gida har sai ya je ya ga Fatima. Don haka ko da ya shiga gidan Fatima, sai Ali (a.s) ya masa bushara da wannan karuwa da aka yi ya kuma kawo masa abar haihuwar yana mai bukatarsa da ya sanya mata suna, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya amsa masa da cewa: Lalle ba zan gabaci Ubangijina ba wajen sanya mata suna. A daidai wannan lokaci sai ga Mala’ika Jibrilu (a.s) ya sauko da sakon Ubangiji yana mai ce wa Manzo (s.a.w.a) cewa: “Mai Girma da Daukaka yana isar maka da gaisuwa Yana mai umartanka da ka sanya mata suna Zainab”, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar. Hakan kuwa aka yi, nan take Manzo ya sanya mata suna Zainab. Wasu ruwayoyi sun ce bayan haka kuma sai Jibrilu (a.s) ya sanar da Manzon Allah (s.a.w.a) irin abubuwan da zai faru da ita na wahalhalu da kuma yadda za ta kasance ita kadai a Karbala wajen kare wannan addini da kuma fuskantar makiya Allah wadanda suke son ganin bayan wannan addini bayan shahadar dan’uwanta Husain (a.s).

 

SHARE:
Makala 0 Replies to “Sayyida Zainab al-Kubra ‘Yar Imam Ali (a.s)”