December 16, 2021

Sayyida Fatima al-Zahra (a.s)- Marainiya

Daga Muhammad Awwal Bauchi


 

Manzon Allah (s.a.w.a) ya isar da sakonsa kuma ya kammala aikinsa a wannan doron kasa, don haka lokaci ya yi da zai koma ga Ubangijinsa, inda zai rayu rayuwa mai dorewa cikin ni’ima; don haka sai ajali ya kusance shi.

Sai Manzon (s.a.w.a) ya fara rashin lafiya. Rashin lafiya ya tsananta gare shi, Fatima na kallonsa alhali tana jin cewa ita ke dauke da duk wata damuwa ta duniya.

Wata rana Fatima ta tafi don gai da babanta, ta zo masa cike da bakin ciki har ta kusanci inda yake, sai ya yi mata maraba ya faranta mata rai sannan ya zaunar da ita a kusa da shi, ya ce mata: “Maraba ‘yata”. Sannan ya sanar da ita da kusantar ajalinsa da rasuwarsa; sai ta fashe da kuka. Sannan ya ba ta labarin cewa ita ce farkon wadda za ta fara haduwa da shi daga iyalinsa, sai ta yi dariya saboda farin ciki da haka, abin da ke nuna irin tsananin ta’allakuwarta da Manzon Allah (s.a.w.a); domin ta fifita mutuwa don haduwa da shi bisa rayuwa babu shi.

Ranakun rashin lafiyar Manzo (s.a.w.a) sun ci gaba da tsananta, lamarin da ya sanya musulmi suka shiga cikin halin dar-dar da damuwa, kamar yadda Fatima ma take cikin halin tsananin bakin ciki da damuwa.

Haka dai aka ci gaba har lokacin da Allah Ya yi izini wa ManzonSa (s.a.w.a) da ya tafi zuwa gare shi, Ya zabe shi zuwa makotaka da Shi, wato Allah Ya yi masa rasuwa. Habawa! Ai dan Adam ya shiga wani yanayi na rashi. Kasa ta yi rashin tauraronta na shiriya da rahama. Fatima kuwa ba a magana! Bakin ciki ya tsananta gare ta, saboda haka ta shiga wata sabuwar rayuwa ta damuwa bayan babanta. Ta shiga jiran lokacin da za ta tafi ta rayu tare da shi a Aljanna dawwamammiya.

Fatima ba ta yi tsawon rai bayan Manzon Allah (s.a.w.a) ba, kamar yadda ya gaya mata a baya cewa, ita ce farkon wadda za ta hadu da shi daga iyalinsa. Malumman tarihi sun sassaba a kan tsawon lokacin da ta saura bayan mahaifinta; wasunsu sun ce ta rayu na tsawon kwanaki saba’in da biyar, wasu kuma suka ce ta kai har watanni uku, yayin da wasu suka tafi a kan watanni shida.

Hakika Fatima ta rayu a wannan dan karamin lokaci tana mai hakurin rashi da maraici, ta share su cikin ibada da yankewa ga Allah Madaukaki, kamar yadda ta taka muhimmiyar rawa cikin al’amurran sako da al’uma kamar al’amarin halifanci. Hakika Fatima ta tsaya kyam a gefen mijinta Ali (a.s.) da cancantarsa ga halifanci bayan Manzo (s.a.w.a). Ta kasance tana haduwa da Muhajirai da Ansar tana tattaunawa da su a kan haka. Wannan mawuyacin yanayi ya yi matukar tasiri ga lafiyarta; domin kiri-kiri tana kallon gaskiya na kaucewa daga wajensa, kuma kiri da muzu aka kau da kai daga wasiyyoyin Annabi (s.a.w.a) a kan iyalansa, sai Fatima ta fita daga wadannan fare-fare cikin bakin ciki da yanke kauna.

Wannan kadan ne daga tarin abin da ya sauka a kansu, mun ambaci dan abin da ya dace da wannan matsayin ne.

Sabani ya gudana tsakaninta da Abubakar kan Fadak, wanda wani fili ne na noma da Manzon Allah ya ba ta kyautarsa a lokacin rayuwarsa. A yayin da Manzo ya bar duniya sai Abubakar ya hana ta, ya ki karbar shedar Imam Ali (a.s.) kan cewa mallakarta ne. Wannan ya sa al-Zahra (a.s) ta yi tsananin jayayya da shi, ta kuma yi maganganu masu zafi da ke kunshe a cikin shafukan tarihi. Mallakar wannan gona dai bai dawo ga Ahlulbaiti (a.s.) ba sai a lokacin mulkin Umar bin Abdul-Aziz, wanda ya mayarwa ‘ya’yan Fatima da Fadak.. Amma bayan mutuwarsa mahukuntan Umayyawa sun sake kwace ta.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Sayyida Fatima al-Zahra (a.s)- Marainiya”