September 2, 2023

​ Sayyid Nasrullah Ya Gana Da Shugabannin Hamas Da Jihad Islami

 

Babban sakataren kungiyar Hizbull Sayyed Hassan Nasrallah ya karbi bakuncin babban sakataren kungiyar ta jihad Ziad Nakhalah da mataimakin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Saleh Al-Arouri, inda suka tattauna batutuwan siyasa da soja da kuma ci gaban batutuwan tsaro, da daidaita tsare-tsare tsakanin ƙungiyoyin gwagwarmaya, musamman a Palastinu da Lebanon.

A yau Asabar ne babban sakataren kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah ya karbi bakuncin babban sakataren kungiyar Islamic Jihad Ziad Nakhalah da mataimakin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Saleh Al-Arouri a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon.

A yayin ganawar tasu, Sayyed Nasrallah, Nakhla, da Al-Arouri sun yi nazari kan al’amuran siyasa na baya-bayan nan, musamman a Palastinu a yankunanta da Isra’ila ta mamaye a yammacin kogin Jordan.

Bayanin taron na bangarorin uku ya tabbatar da tsayuwar daka daga dukkan dakarun kungiyoyin gwagwarmaya domin tinkarar ayyukan wuce gonad a iri da mamayar Isra’ila.

A cewar sanarwar hadin gwiwa, an jaddada muhimmancin hada kai da bin duk wani ci gaba na siyasa, tsaro da soja da kuma daukar matakin da ya dace.

 

©Hausa tv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​ Sayyid Nasrullah Ya Gana Da Shugabannin Hamas Da Jihad Islami”