September 26, 2021

Sayyid Ali khamnei (DZ) ya jagoranci sallan jana’izan babban Malami Ayatullah Sheikh Hassan Zada Amuli (R)

Daga Imran Darussalam


A yammacin yau lahdi 26/9/2021 ne Jagoran juyin juya hali kuma babban Marji’in nan na addini Sayyid Ali Khamnei (DZ) ya jagoranci sallata jana’izan Sheikh Hassan zada Amuli, bayan ya jagoranci sallan tare da karanta fatiha ga ruhinsa sai yayi bankwana da jikin mamacin mai tsarki.

Sakon Sayyid Ali Khamnei (DZ) na ta’aziyyan Sheikh Hassan Zada Amuli.

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai.
Ina mika ta’aziyyata dake cike da damuwa da alhini na rashin wannan mabubbuga kuma malami Ayatullah Sheikh Hassan Zada Amuli Allah ya gafarta masa.
Wannan Sheikh ya kasance babban masani ne, kuma masanin fannoni dayawa na ilimi, Shi mutum ne da da wuya ake samun irin su a kowane zamani abin alfaharin mu, tabbas rubuce rubucen wannan mutum mai girma zata zamto mabubbuga mai tsarki ga ma’abota ilimi insha Allah.

Ina mika sakon ta’aziyya ga dukkan abokan shi da daliban shi dama masoyan shi, Musamman ga Ahalin Amuli muminai.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Sayyid Ali khamnei (DZ) ya jagoranci sallan jana’izan babban Malami Ayatullah Sheikh Hassan Zada Amuli (R)”