January 5, 2024

Sayyedah zahra a.s ajiyar Allah a Bayan Kasa yar ma,aikin Allah s.a.w.a

Ankarbo Daga Mufdil Bin Umar {R} Cewa Ya tambayi Imamuss-Sadiq {A} Yaya Haihuwar Sayyadah Fatimah {S} Ya Kasance? Sai Yace: { Na’am Lallai Sayyidah Khadijah Yayinda Ta Auri Manzon Allah {S} Matan Quraishawa Sun Qaurace Mata Basa Shiga Gidanta Basa Yimata Sallama Kuma Basa Barin Wata Mace Ma Tashiga Gidanta, To Sai Sayyidah Khadijah As Ta Damu Dangane Da Hakan, Bayan Tadauki Cikin Sayyidah Fatimah, Sai Ta Kasance Suna Magana Da Ita Tun Tana Cikinta, Tna Bata Haquri Akan Abunda Matana Quraishawa Suke Mata, Sayyidah Khadijah Ta Kasance Tana Boye Wannan Hirar Dasuke Yi Da Diyarta, Harsaida Wata Rana Manzon Rahama {S} Ya Shigo Yaji Sayyidah Khadija Tana Magana Da Sayyidah Fatimah {S} Saiyace Da’ita: Yakhadijah Wake Magana Dake ? Sai Tace: Jarin Dake Cikina Shike Magana Dani Mukeyin Hira, Sai Yace Da Ita Ga Mala’ika Jibrilu {S} Nan Yana Min Bushara Cewa Lallai Maca Ce Tsarkakakkiya, Kuma Allah Tabaraka Wata’ala Zai Sanya Tsatona Daga Wajanta Kuma Zaisanya Daga Tsatsonta Shugabanni A Wannan Al’ummar Yasan Yasu Halifofi A Doran Qasar Sa Bayan Yankewar Wahinsa.

Darajojinta:

1- Shugabar Matan Duniya Da Lahira.

2- Diyar Manzon Rahama Wanda Babu Tamka Tasa Duniya Da Lahira.

3- Matar Imam Ali {S} Wanda Yake Annabwa Suke Kabar Karatu Tawajansa Kuma Da Shine Allah Ya Ke Taimakon Su. Wajan Isar Da Saqonsa.

4- Mahaifiyar Shugabannin Aljannah Da Kuma Duniya Da Lahira.

5- Wacce Aka Daura Auran Ta A Sama Da Kwana Arba’in Kana Aka Daura A Qasa Da Sadaki Dirhami 480. Tana Shekara Tara.

6- Wacce Allah {S} Keyin Fushi Da Fushinta Yake Yarda Da Yardarta.

7- Ita Ce Wacce Aka Sherawa Manzon Allah Damuwa Da Tsangwama Da Haihuwarta.

8- Wacce Allah {S] Yab ada Auranta, Mala’ika Jibrilu {S} Manemin Auranta, Mala’ika Maika’il Da Israfil {S} Da Mala’iku Dubu Saba’in Sune Shaidar Daurin Aurenta.

9- Itace Yar’ Annabi, Matar Imam Ali {S] Mahaifiyar A’immah {S}.

10- Itace Wacce Allah Zai Fara Yin Hukunci Ga Wadan Da Suka Zalunce Ta Da Ya’ayanta.

SAYYIDA ZAHARA (AS) AJIYAR ALLAH (T) A CIKIN HALITTARSA!

1. Manzon Allah (S) Yana Cewa: ”Da Ace Kyau Mutum Ne To Da ‘Fatima’ Ne Hakika Diyata Fatima Tafi Duk Halitta Kyawun Usuli Da Daukaka (Faraidus-Simdaini,J,01,S,68).

(2). Imam Hasanul Mujtaba (As) Yana Cewa: ”Naga Mahaifiyata Fatima Tana Sallah A Daya Daga Cikin Dararen Juma’a Ba Ta Gusheba Tana Mai Yin Ruku’u Da Sujjada Har Safiya Ta Yi Naji Tana Wa Muminai Maza Da Mata Addu’a Amma Banji Ta Rokawa Kanta Wani Abu Ba. Sai Nace Mata: Umma! Saboda Mi Ba Ki Wa Kanki Addu’a Ba Kamar Yadda Na Ji Kinawa Waninki? Sai Tace Ya Dana! Anawa Nakusa Ne Addu’a Sannan Na Cikin Gida” (Biharil-Anwar,J,43,S,81).

(3). Daga Imam Husain (As) Annabi (S) Yana Cewa: ”Fatima Sanyin Zuciya Ta Ce,’Ya’yanta Masu Faranta Zuciya Ta Ne, Mijinta Hasken Idanu Na Ne, ’A’imma Daga Tsatsonta Amintattun Ubangiji Na Ne, Igiyar Allah Ne Tsakanin Sa Da Halittarsa, Wanda Ya Rike Su Ya Tsira, Wanda Ya Ki Su Ya Halaka. (Faraidus-Simdaini,J,2,S,66)

(4). Imam Sajjad (As) Yana Cewa: ”A Lokacin Da Musulumci Ya Zo Fatima Ce Diyar Da Kadijah As Ta Haifawa Annabi (S). (Raudatil-Kafi,536)

5. Imam Bakir (As) Yana Cewa: ”An Ambaci Fatima Bnt Muhammad Da (Dahira) Saboda Ita Tsarkakkiya Ce Daga Dukkanin Datti, Ba Ta Taba Yin Jini Ba ( Na Haila Ko Nifasi). (Bihar,J,43,S,19)

(6). Imam Kazeem (As) Yace: ”Tabewa Ba Ta Shiga Gidan Da Ya Ke Akwai Mai Sunan Muhammad Ahmad Ali Hasan Husain Da Mace ‘Fatima (As). (Safinatul-Bihar,J,01,S,662).

(7) Imam Jawad (As) Yace: Annabi (S) Yana Cewa: ”Ana Kiran Diya Ta Da “Fatima” Ne Saboda Allah (T) Ya Tseratar Da Ita, Da Dukkanin Wanda Ya Sota Daga Wuta. (Ulumul Wal,Ma’arif,J,6,S,30).

(8). Imam Hasanul-Askari (As) Yana Cewa: ”Ana Kiran Fatima Da (Zahra’u) Ne, Saboda Fuskar Ta Tana Yin Haske Ga Amiril Muminin (As) Da Safe Kamar Rana, A Yayin Zawali Kamar Wata, A Yayin Faduwar Rana Kamar Tauraro Mai Haske (Awalimul-Ulum,J,6,S,33).

(9). Daga Imam Rida Daga Kazeem Daga Sadeeq Daga Bakir Daga Sajjad Daga Husain (As), Daga Ali Bn Abi Dalib (As), Daga Manzon Allah (S) Yana Cewa: ”Ban Aurar Da Fatima Ba, Har Sai Da Allah (T) Ya Umar Ce Ni Da Hakan”. (Musnadi Imam Rida (As).

(10). Daga Fatima ‘Yar Rida Daga Fatima ‘Yar Sadeeq Daga Fatima ‘Yar Bakir Daga Fatima ‘Yar Sajjad Daga Fatima ‘Yar Husain Daga Zainab Bnt Amiril Muminin (As) Daga Fatima Bnt Muhammad (S) Manzon Allah (S) Yace: ”Wanda Ya Bar Duniya Akan Kaunar Ali-Muhammad, Ya Rasu Yana Shahidi (Awalimul-Maarif,J,21,S,354).

SHARE:
Makala 0 Replies to “Sayyedah zahra a.s ajiyar Allah a Bayan Kasa yar ma,aikin Allah s.a.w.a”