September 26, 2023

Saudiyya Ta Yi Tir Da Yadda AKe Tada Zaune Tsaye A Masallacin Kudus

 

Saudiyya, ta yi tir da Allah-wadai da yadda masu tsatsauran ra’ayi ke ci gaba da tada zaune tsaye a masallacin Kudus, bisa samun kariyar jami’an tsaron Isra’ila.

Ma’aikatar harkokin wajen Masarautar ta bayyana nadama kan yadda mahukuntan Isra’ila ke keta kokarin zaman lafiya na kasa da kasa, da ya shafi girmama wuraren ibada.

Ma’aikatar ta jaddada matsayar Masarautar na goyon bayan al’ummar Falasdinu da duk wani mataki na kawo karshen mamayar da Isra’ila ke yi a yankunan Falasdinawa.

Har ila yau, ta bayyana goyon bayanta ga samar da adalci ga al’ummar Falasdinu na samun damar kafa kasarsu mai cin gashin kanta bisa tanadin iyakokin shekarar 1967, tare da gabashin Kudus a matsayin babban birninta.

 

©HTV

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Saudiyya Ta Yi Tir Da Yadda AKe Tada Zaune Tsaye A Masallacin Kudus”