April 20, 2023

Saudiyya Ta Yi Shirin Duban Watan Sallah

Saudiyya ta kammala shirin duban watan sallah a wannan Alhamis din.

Shirin na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Musulmi suka dauki azumi na 29.

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da mahukunta Masallatan Harami na Makkah da Madina suka fitar a Twitter.

Shafin na Haramain Sharifain ya bayyana cewa daga yau Alhamis za a fara duban watan na Shawwal.

An girke manyan na’urorin hangen nesa domin aikin duban watan Shawwal.

Ana sa ran fara duba watan Shawwal ne a birnin Sudair da misalin karfe 06:09 na yamma, sai garin Tumair inda za a fara duba da 06:22 na dare.

A nan gida Najeriya ma, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bukaci al’umma su fara duban jaririn watan Shawwal daga yau Alhamis 29 ga watan Ramadan.

 

©Aminiya

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Saudiyya Ta Yi Shirin Duban Watan Sallah”