Saudiyya ta raba kayan tallafi ga waɗanda ta’addanci ya ɗaiɗaita su dubu 16 a Borno

Magidanta 16,000 da ke fama da tashe tashen hankula a Borno sun sami tallafin kayan agaji da gwamnatin Saudiyya ta bayar.
Tallafin dai shi ne karo na uku da mahukuntan Saudiyya suka bayar ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a Borno ta hannun cibiyar agajin jin kai ta Sarki Salman.
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ce ta raba kayan tallafin.
A sakonsa na rabon kayayyakin da aka gudanar a yau Alhamis a sansanin ƴan gudun hijira na Muna Kumburi, Darakta Janar na NEMA, Mustafa Habib, ya ce an bayar da irin wannan tallafi ga wadanda abin ya shafa a Yobe da Zamfara.
Habib ya samu wakilcin Hajiya Fatima Kassim, mukaddashiyar daraktar tsare-tsare ta hukumar.
“Cibiyar ta ba da gudummawar kayan abinci buhuna 16,000 na kayan agaji ga gidaje 16,000 a jihar Borno don zagaye biyu na gidaje 8,000 kowanne a sansanoni daban-daban, a cikin Disamba 2022.
“Kowane gida ana sa ran samun kwandon abinci mai nauyin kilogiram 59.8 wanda ya kunshi kilogiram 25 na shinkafa; 25 kg na wake; 4 kilogiram na gari Masavita, 2 kilogiram na tumatir manna; lita na man gyada; 1kg na gishiri da 0.8kg na maggi cubes.
“Wannan kashi na biyu zai gudana ne a sansanin Muna Kumburi, Gongulon, Madinatu I da Madinatu II,” in ji Habib
©vDaily Nigeria