May 10, 2023

​Saudiyya Ta Dawo Da Dukkanin Huldodi Na Diflomasiyya Tare Da Syria

 

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta sanar da cewa, Masarautar ta yanke shawarar ci gaba da gudanar da ayyukanta na diflomasiyya a kasar Siriya.

A cikin bayanin da ma’aikatar harkokin wajen Saudiyyar ta fitar ta ce: wannan matakin yana zuwa bisa alakar ‘yan uwantaka da ke hada kan al’ummar masarautar Saudiyya da Jamhuriyar Larabawa ta Siriya, da kuma nuna sha’awar bayar da gudummawa ga ci gaban ayyukan hadin gwiwa na kasashen Larabawa, da inganta tsaro. da kwanciyar hankali a yankin, da kuma la’akari da shawarar da taron ministoci na majalisar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa ya fitar, wanda aka gudanar a birnin Alkahira a ranar 7 ga watan Mayun 2023, na ci gaba da halartar tawagogin jamhuriyar larabawan kasar Syria a taron koli na Majalisar.

Da kuma aiki tare a dukkanin Tarurrukan majalisar kungiyar kasashen Larabawa da dukkanin kungiyoyi da sassan da suke da alaka da su, tare da bin ka’idojin tsare-tsare na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa, da alkawura da ka’idoji na kasa da kasa, a bisa wannan masarautar Saudiyya ta yanke shawarar cewa; za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na diflomasiyya a Jamhuriyar Larabawa ta Siriya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Saudiyya Ta Dawo Da Dukkanin Huldodi Na Diflomasiyya Tare Da Syria”