September 24, 2021

Saudiyya: Dole A Haramtawa Iran Mallakar Makamin ‘Kare-Dangi

Daga Musa Isah Saleh


Masatautar saudiyya ta nuna damuwarta kan halin da yankin Gabas ta tsakiya zata tsinci kan ta idann aka halastawa kasar Iran mallakar makamin kare-dangi.

Sarkin saudiyya Salman Bin Abdulaziz ne yayi wannan kiran a ranar Alhamis 23 ga watan Satumbar 2021 a yayin gabatar da jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) wanda aka gabatar a garin Newyok da ke kasar Amurka.

Sarkin ya bayyana cewa baiwa kasar Iran damar makaman ko kuma kera su babban kalubale ne ga daukacin yankin gabas ta tsakiya duk da kuwa kasar ta nuna cewa zata mallaki makamin ne ba da niyyar cutar da kowa ba, Sarkin ya bayyana cewa kasar Saudiyya na shirye don bada goyon bayan dakatar da Iran daga aniyar ta.

Ya kara da cewa kasar sa za ta cigaba da kalubalantar duk kungiyoyi masu tsastsauran ra’ayi wanda aka gina su bisa tsana, ya ce kasar sa na gaba-gaba wurin fada da kungiyoyin ta’addanci da masu tsauraran ra’ayoyi. Kama kuma yace suna tare da kasashen da ke tsayin daka wurin yakar masu nuna goyon baya ko daukar nauyin kungiyoyin ta’adda.

Sarkin ya bayyana dalilan sa na cigaba da yaki da rundunar Houthi na kasar Yemen, inda yace yan Houthi sun ki aminta da duk hanyoyin sulhu da saudiyya ta zo musu da shi. A bangare guda kuwa yan Houthi na ganin hare-haren saudiyya kan kasar su Yemen matsayin cin zali, kana kuma sun nuna cewa sharrudan yarjejeniyar da Saudiyya ta zo musu da shi ya kasance bisa son rai.

A bangaren annobar Korona kuwa, Sarki Salman ya bayyana cewa kasar sa ta bada tallafin dalar Amurka miliyan Dari Biyar ($500) a kokarin da duniya tayi na fuskantar annobar, Kana kuma ta bada tallafin dala miliyan 300 don tallafawa kasashen da ke kokarin yaki da cutar.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Saudiyya: Dole A Haramtawa Iran Mallakar Makamin ‘Kare-Dangi”