January 12, 2023

Sarkin Kano Ya Naɗa Sabon Limamin Masallacin Marigayi Dr Ahmad Bamba

Jaridar Internet Alfijr ta rawaito cewa, mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada Dr. Malam Umar Ibrahim Indabawa  a matsayin sabon limamin  Masallacin Darul hadis dake Unguwar Tudun Yola a Karamar  Hukumar Gwale.

Hakan ya biyo bayan hayaniya da hargitsi da ya tashi ranar Juma’a yayin gabatar da sallar Juma a, wanda hakan ta janyo rufe masallacin.

Haka zalika mai martaba sarkin na Kano ya kuma yi kira ga masu neman kujerun mulkin kasar nan da su tabbatar sunyi kalamai da al’umma za su gamsu da su wajen neman kuri’ar alumma a zaben shekarar 2023.

Sarkin ya bayyana haka ne lokaci da dan takarar shugaban kasa na jam’iyar SDP Adewale Adebayo da dantakar kujerar gwamnan jihar Kano Dr. Muhammad Bala gwagwarwa, su ka  ziyar ce shi a fadar sa.

Alhaji Aminu Bayero, ya ce, duk wani dake neman kujerar da yasan cewa Allah ne ke bayarwa ya kamata ya guji tada zaune tsaye.

Dayake nasa jawabin, dan takarar Gwamna na jam’iyyar ta SDP Bala Muhammad Gwagwarwa, ya ce, sun ziyarci fadar sarkin ne domin neman tabarraki da addu’arsa.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sarkin Kano Ya Naɗa Sabon Limamin Masallacin Marigayi Dr Ahmad Bamba”