October 26, 2021

Sarkin BirninGwari – Katse hanyoyin sadarwa ya rage tasirin ‘yan bindiga

Daga Danjuma Makeri


A wani rahoto da ya zo mana daga jihar Kaduna, a yayin gudanar da wani taro da aka shirya a jihar, Sarkin garin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril MaiGwari ya bayyana cewa katse layukan wayoyi ya rage tasirin ‘yan bindigan da ke addabar al’ummar jihar ta Kaduna.

Sarki Zubairu ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da ma’aikatar harkokin tsaro na cikin gida ta shirya a jihar.

Ya kuma kara da cewa matakan da gwamnatin jihar ta dauka don dakile matsalolin tsaro a jihar na tasiri kuma yana haifar da sakamako mai kyau a karamar hukumar Birnin Gwari
A fadin sarkin, farmakin da jami’an tsaro ke gudanarwa kan yan bindigan a yankin Zamfara ya haifar tilasta musu yin hijira zuwa wasu sassan karamar hukumar Birnin Gwari.

Bayyanar su a yankin kuma ya haifar da tilastawa manoma dakatar da ayyukan noma a gonakin su. Ya zuwa yanzu, in yan bindigan suka yi garkuwa da mutum sukan tambayi abinci a madadin kudin fansa da suka saba tambaya a da.

Kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa matakan da suka dauka din na bisa shawarwarin jami’an kula da kuma dakile ayyukan ta’addanci a kokarin su na yaki da yan bindigan.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Sarkin BirninGwari – Katse hanyoyin sadarwa ya rage tasirin ‘yan bindiga”