Saraya Kudus: HKI Ta Aikata Laifin Yaki A Kan Al-Ummar Falasdinu A Yau

Kakakin rundunar Saraya Kudus ta kungiyar Jahadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye ya bayyana cewa a safiyar yau gwamnatin HKI ta aikata kissan kiyashin da ya kai laifin yaki ko kuma take hakkin bil’adama mafi muni a harin da ta kai yankin zirin Gaza a safiyar yau Talata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Abu Hamza yana fadar haka a yau Talata, ya kuma kara da cewa jinin Falasdinawan da HKI ta kaisu ga sahada a safiyar yau zai kara karfafa Falasdinawa ne a gwagwarmayan da suke yi da ita.
Kakakin dakarun Saraya Kudus ya yi kira ga Falasdinawa su goyi bayan gwagwarmayan da dakarunsu suke yi da HKI su kuma gano cewa gwagwarmaya da makami it ace kawai hanyar fuskantar ta’asar da HKI take aikatawa a cikin al-ummar Falasdinu. Sannan ya kammala da cewa dakarunsa zasu ci gaba da tafarkin gwagwarmaya da HKI har zuwa nasara da yardar All…
A safiyar yau Talata ce jiragen yakin HKI suka kai hare-hare ta sama kan yankin Zirin Gaza inda suka kashe falasdinawa akalla 13 daga cikinsu akwai kwamandojin dakarun Saraya Kudus 3, yaea 4 sannan wasu kimani 20 suka ji rauni