April 9, 2024

Sanarwan Ganin Wata Daga Ofisoshin Wasu Marji’an Shi’a

Sanarwan Ganin Wata Daga Ofisoshin Wasu Marji’an Shi’a.

Ofishin Babban Marji’i Ayatullah Sayyid Ali Sistani (DZ) da Sayyid Ali khamene’i (DZ) da Ayatullah Sayyid Kamal Haudari (DZ) da ofishin Sayyid Sadiq Shirazi (DZ) da ofishin Sheikh Muhammad Ya’aqubi (DZ) da ofishin Sayyid Hussain Fadlullah (QS) da ofishin Sayyid Muhammad Taƙi Mudarrisi (DZ) da ofishin Ayatullah Baghdadi (DZ).

Duka sun fitar da sanarwan cewa gobe Laraba da yayi daidai da 10 ga watan Afrilu shine ranar 1 ga watan shawwal wato ranar idin karamar sallah.

Allah madaukakin sarki ya maimaita mana, ya karɓi ibadunmu.

Amjad Mukhtar Imam

 

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sanarwan Ganin Wata Daga Ofisoshin Wasu Marji’an Shi’a”