March 2, 2024

Sana’a ta harba makamai masu linzami 384 da jirage marasa matuka kan jiragen ruwa a tekun Bahar Rum

Shugaban Ye-meni An-sar All-ah ya sanar da cewa, Sana’a ta harba makamai masu linzami 384 da jirage marasa matuka kan jiragen ruwa a tekun Bahar Rum da ke kan hanyar da Isra’ila ta mamaye na Falasdinu zuwa yanzu.

A lokacin da yake tsokaci kan hare-haren da Amurka da Birtaniya suka kai kan kasar Yemen, shugaban na Yemen ya dage cewa wadannan hare-haren ba su shafi karfin sojan Dakarun ta kowace fuska ba.

Ya ci gaba da bayyana cewa makiyan kasar Yemen suna bayar da gudunmawa wajen ci gaba da bunkasa karfin soji na Dakarun.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sana’a ta harba makamai masu linzami 384 da jirage marasa matuka kan jiragen ruwa a tekun Bahar Rum”