March 5, 2023

Samun ci gaba mai dorewa a Afrika na bukatar amfani da karfin kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire.

Wasu masana sun jaddada cewa, samun ci gaba mai dorewa a Afrika na bukatar amfani da karfin kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, wajen magance matsaloli a bangarori daban-daban.
Wata sanarwa da hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika (UNECA) ta fitar a ranar Juma’a, ta ruwaito masanan na bayyana haka ne yayin wani taro kan kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, da ya gudana a ranar Alhamis a Niamey na Niger, a gefen taron nahiyar kan ci gaba mai dorewa, karo na 9, wanda ya gudana a zahiri da kuma kafar intanet.
A cewar hukumar UNECA, masanan sun jaddada muhimmancin rawar da kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire za su taka wajen tabbatar da ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a da magance matsalolin sauyin yanayi da ma kare muhalli.
Har ila yau, sun nanata bukatar karfafa amfani da kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire a fannin raya muhallin mabambantan halittu, ta hanyar inganta kirkire-kirkire da sana’o’i da zuba jari a fannin bincike da samar da ci gaba.
Masanan sun yi ammana cewa, nahiyar na iya amfani da kimiyya da fasaha wajen gaggauta ci gaban tattalin arziki da zamantakewa da cimma muradun ci gaba masu dorewa na MDD da ake son cimmawa zuwa shekarar 2030, har ma da cimma ajandar ci gaba ta shekarar 2063, ta Tarayyar Afrika AU.

©cri Hausa (Fa’iza)

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Samun ci gaba mai dorewa a Afrika na bukatar amfani da karfin kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire.”