December 1, 2022

Sama da Amurkawa miliyan 1.11 ne suka mutu sakamakon harbin bindiga a cikin shekaru 32 da suka gabata.

Sama da Amurkawa miliyan 1.11 ne suka mutu sakamakon harbin bindiga a cikin shekaru 32 da suka gabata
Wani sabon rahoton bincike da mujallar The Journal of the American Medical Association ta bayar na baya-bayan nan, ya nuna cewa, daga shekarar 1990 zuwa 2021, sama da mutane miliyan 1.11 suka mutu, sakamakon tashe-tashen hankali masu nasaba da harbin bindiga a Amurka, inda kashi 25.8 cikin dari na wadanda abin ya shafa bakaken fata ne ‘yan asalin Afirka. Binciken ya nuna cewa, akwai bambanci sosai na yawan mace-macen dake da alaka da harbin bindiga a tsakanin kabilu daban daban a Amurka, kuma bambance-bambancen ya kara fitowa fili a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Binciken ya kuma bayyana cewa, adadin mace-macen dake da nasaba da harbin bindiga a Amurka, ya kai matsayin koli a shekarar 2021 a cikin shekaru 30 da suka wuce.

©cri (Safiyah Ma)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sama da Amurkawa miliyan 1.11 ne suka mutu sakamakon harbin bindiga a cikin shekaru 32 da suka gabata.”