April 19, 2023

Sallah: NSCIA ta kafa kwamitin ganin wata

 

Majalisar ta bukaci al’ummar Musulmi a fadin kasar nan da su sanya ido kan sanarwar da Sarkin Musulmi zai yi a daren Alhamis 20 ga watan Afrilu.

Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya NSCIA a karkashin jagorancin shugabanta kuma mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ta sanar da kwamitin ganin watan Shawwal – wanda zai kawo karshen azumin watan Ramadan.

Hukumar ta NSCIA ta kuma taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar bukukuwan Sallah mai zuwa, inda ta bukace su da su raba wa mabukata Zakkatul Fitr a kan lokaci.

Hukumar NSCIA a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun Daraktanta na gudanarwa, Zubairu Usman-Ugwu, ta ce majalisar ta roki Allah da ya ba kowa damar shaida bukukuwan Sallah.

SHARE:
Tarbiyyan Yara 0 Replies to “Sallah: NSCIA ta kafa kwamitin ganin wata”