September 25, 2021

Sakon Ta’aziyya

 

JARIDAR AHLULBAITI (AS) take mika sakon ta’aziyya da alhini ga iyalen Malam Auwal Bauchi bisa babban rashi da mukayi na wannan mutum mumini mai kokari (wanda zamu iya cewa daya yake tamkar dubu).

 

A janibi guda kuwa wannan jarida taku mai albarka take karkatar da alkalaminta zuwa mika sakon ta’aziyya ga sauran ‘yan uwa musulmi, wanda wannan rashi ba ya shafi iyalan shi kadai bane, ya shafi dukkan ‘yan uwa musulmi.

 

Malam Auwal Bauchi ya kasance mutum na mutane, ga iya mu’amala da sanin yakamata, Marigayin Malam Auwal Bauchi mutum ne da bai yarda da ‘bangaranci ba bare kuma ta’assubanci.

 

Idan muka leka bangaren rubuce rubuce, Marigayin ya fassara litattafai masu tarin yawa duka dan amfanin ‘yan uwa musulmi, ya bada lokacin shi da yin aiki tukuru wajen isar da sako da hidima wa wannan Mazhabi na Imamai sha biyu.

 

Haka zalika marigayin ya kasance tsayayyen dan jarida mara tsoro mai iya bincike da bayyana gaskiya a duk inda ya samu kanshi.

 

Muna rokon Allah ya jikan shi, ya gafarta masa, ya sada shi da Manzo da Ahlulbaiti Allah ya kara musu yarda.

SHARE:
Tarbiyyan Yara 0 Replies to “Sakon Ta’aziyya”