August 18, 2021

Sakon Ta’aziyya Da Jan Hankali Ga Al’umma Da Gwamnatin Najeriya

Amadadin shugaban Mu’assasar shi’a wato  Rasulul A’azam Foundation (RAAF) ta kasa mai cibiya a Kano, Hujjatul Islam Shaikh Muhammad Nura Dass, yana mika sakon ta’aziyya ga shugaba a ɗarikar Tijjaniyya, Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi (H) da ƴan ɗarikar Tijjaniyya da ɗaukacin al’ummar ƙasa baki ɗaya dangane da kisan gillar da aka yi wa ƴan’uwa musulmi a garin Jos, bayan kammala taron zikiri na murnar shigar sabuwar shekarar musulunci ta 1443.
Muna fatar Allah Ya jikan su da rahamarSa, Ya kuma bada hakurin jure wannan babban rashi.
Sannan shugaban na wannan mu’assasar yana kira ga al’umma da a kai zuciya nesa, kada a dauki doka a hannu, sannan kuma yana kira ga gwamnati da ta bibiyi lamarin kuma ta hukunta waɗanda suke da hannu a kan wannan aika-aika domin ya zama darasi ga masu niyyar yin irinsa nan gaba.
Daga ƙarshe shugaban mu’assasar yana amfani da wannan dama wajen kira ga gwamnati da ta ƙara kaimi wajen ɗaukan mataki game da lamarin tsaro tun a matakin farko, ta bibiya ta magance shi kafin ya haɓaka, domin wannan ta’addancin da ya faru sakamako ne na rikicin da ke faruwa tsakanin wadannan mutane mazauna yankin tare da fulani makiyaya.
Allah Ta’ala Ya zaunar da kasarmu lafiya tare da yalwar arziki.
Daga Jamiin hulɗa da jamaa (P.R.O)
Murtala Isah Dass
17/8/2021
SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sakon Ta’aziyya Da Jan Hankali Ga Al’umma Da Gwamnatin Najeriya”