October 19, 2023

SAKON NUNA GOYON BAYA GA FALASDINAWA DA BARRANTA DAGA ZALUNCIN YAHUDAWAN HARAMTACCIYAR KASAR ISRA’ILA

Daga: Muassasar Rasulul A’azam (RAAF) ta Kasa

Wannan mu’assasa tana bayyana goyon bayanta a fili ga yan’uwa al’ummar Falasdinu game da gwagwarmayar kwatan yancin zaluncin mamayar fin karfi da yahudawan Isra’ila suke yi musu da ma walakanci da dauri har da kisan da kullum suke musu.

 

Wannan mu’assasa tana jinjina wa sauran musulmin duniya da ma wadanda ba musulmi ba, da suke nuna goyon baya da karfafawa ga wadannan tsirarun al’umma na Falasdinu, wadanda manyan kasashen duniya suka zuba ido har ma da nuna goyon baya a akan wannan zalunci.

 

Jinjina ta musamman ga kasar Jamhuriyar musulunci ta Iran da dakarun kungiyar Hizbullahi na kasar Lebanon, wadanda babu tsoro suke nuna izzar musulunci wajen taimakawa ga wadannan miskinai da ake zalunta.

 

Wannan guguwar yaki da ta taso a wadannan kwanaki, muna rokon Allah Ya sanya ya zamo sanadiyyar samun yancin wadannan yan’uwa namu na Falasadinu, ta kuma yantar da Masallacin Baitul Mukaddas.

 

Kuma muna rokon ya zamo shine sababin gushewar wannan azzalumar kasa da masu goya mata baya.

 

Wannan mu’assasa tana allawadai da harin da isra’ila ta kai a asibitin Maamadani wanda ya yi sanadiyyar Shahadar falastinawa sama da dari biyar (500), tana kuma kara tunatar da al’ummar musulmi wajabcin nuna goyon baya da taimakawa ko da da addu’o’i ne.

 

Muna rokon Allah Ta’ala Ya rusa zalunci da azzalumai ko da a zahiri sune masu karfi, ya ba da nasara ga masu gaskiya ko da a zahiri su ne raunana.

 

Daga;

Jami’in Hulda da Jama’a (P.R.O)

Murtala Isah Dass

 

18/10/2023

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “SAKON NUNA GOYON BAYA GA FALASDINAWA DA BARRANTA DAGA ZALUNCIN YAHUDAWAN HARAMTACCIYAR KASAR ISRA’ILA”