June 7, 2024

Sakon Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci Muhammad Sa’ad Abubakar

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana ranar Juma’a 7 ga watan Yuni, 2024 a matsayin ranar 1 ga watan Zulhijja 1445H.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Sultanate Council Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto ya fitar.

Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Juma’a 7 ga watan Yuni 2024 a matsayin ranar daya ga watan Zulhijjah 1445AH da Lahadi 16 ga watan Yuni wanda yayi daidai da 10 ga Zulhijja a matsayin Idin El-Kabir na wannan shekara.

Sultan Sa’ad ya taya al’ummar musulmi barka da Sallah tare da yi musu fatan Allah ya shiryar da su, da albarka da kuma rokon muminai da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, ci gaba da ci gaban kasar, tare da yi wa ‘yan Nijeriya barka da Sallah.

Fassarar:Aishatu Abubakar

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sakon Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci Muhammad Sa’ad Abubakar”