June 3, 2024

Sakamakon karshe a zaben kasar Afrika ta Kudu ya tabbatar da cewa jam’iyyar ANC ta rasa rinjaye

Sakamako na karshe na zaben da aka yi a Afirka ta kudi  a ranar Laraba ya tabbatar da cewa jam’iyyar African National Congress (ANC) ta rasa rinjayenta a karon farko cikin shekaru 30 na cikakkar dimokuradiyya,

Jam’iyyar ANC wadda ta jagoranci yakin ‘yantar da Afirka ta Kudu daga mulkin wariyar launin fata, ta samu kujeru 159 kacal a cikin ‘yan majalisar dokokin kasar mai wakilai 400 bisa kuri’u sama da kashi 40 cikin dari. Babban matsalar rashin aikin yi,Rashin  wutar lantarki, munanan laifuka da kuma rugujewar ababen more rayuwa sun taimaka wajen faduwar Anc.

Daga:Anass Ahmed

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sakamakon karshe a zaben kasar Afrika ta Kudu ya tabbatar da cewa jam’iyyar ANC ta rasa rinjaye”