August 31, 2023

​ Sakamakon Dumamar Yanayi A Duniya Za A Iya Fuskantar Rasa Rayuka

Asusu bayar da lamuni na duniya IMF ya yi gargadin cewa matsalar dumamar yanayi na barazana ga matalautan kasashe, wanda idan har ba a dauki matakan gaggawa ba, za ta fara haifar da asarar rayuka nan da shekarar 2060.

Bayanin ya ce za a samu karuwar kaso 8.5 na adadin rayukan da za a yi asara, musamman a yankunan da ke fama da matsalar sauyin yanayi, kuma kaso 14 na wadannan kasashe za su fuskanci karuwar tsananin zafi.

Daga cikin kasashe 39, wandanda ke dauke da kusan mutane biliyan guda na al’ummar duniya, rabi daga cikinsu da ke fama da wannan matsala sun fito ne daga nahiyar Afirka.

Sama da mutum miliyan 50 ne a wadannan kasashe za su fuskanci tsananin yunwa a 2060, saboda kalubalen da ka iya dabaibaye hanyoyin samar da abinci da kuma hauhawar farashin kayayyaki.

Bayanin ya ce nan da shekarar 2040, wadannan kasashe za su iya fuskantar yanayin zafi sama da digiri 35 a ma’aunin celcius kwatankwacin na kwanaki 61 a shekara fiye da sauran kasashe.

 

©voh

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “​ Sakamakon Dumamar Yanayi A Duniya Za A Iya Fuskantar Rasa Rayuka”