October 8, 2021

Sahabin Manzo, Abu Zar al-Giffari (R.A)

Daga Muhammad Awwal Bauchi


Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Asalin sunansa shi ne Jundub bn Junadat dan kabilar Gaffar shi ya sa ma ake ce masa Al-Gaffari.

Tarihi bai tabbatar da takamammen lokacin da aka haife shi ba, sai dai abin da yake a fili shi ne cewa an haife shi da shekaru masu yawa kafin bayyanar Musulunci saboda ya tsufa sosai lokacin rasuwarsa.

Dangane da lokacin musuluntarsa kuwa malaman tarihi sun tafi kan cewa yana daga cikin na farko-farko, an ce shi ne na hudu ko na biyar cikin wadanda suka fara musulunta.

Abu Zar dai mutum ne da aka sanshi da jarunta, don kuwa lokacin da ya musulunta, duk da cewa a lokacin wadanda suka musulunta suna boye imaninsu saboda cutarwa, amma Abu Zar ftowa fili ya yi a dakin Ka’aba, duk da cewa manyan kafiran Makka suna gurin, ya ce: “Na shaida babu abin bautawa sai Allah, Muhammadu kuma ManzonSa ne. Wannan sanarwa ta Abu Zar dai tana a matsayin bude sabon shafi na fuskantar gumaka da azzaluman shugabanni na lokacin.

Bayyanar da musuluncinsa ke da wuya sai jama’a suka fada masa, masu bugu na yi, masu zagi na yi, sai dai duk da haka abin da ke fita a bakinsa shi ne ‘Kalmar Shahada’.

Haka dai suka ci gaba da azabtar da shi har lokacin da wani mutum daga cikinsu ya kwato shi lokacin da ya shaidawa Kuraishawa cewa: za ku kashe wannan mutumin alhali kuna bin ta hanyar Gaffar kowani lokaci’ (wato akwai yiyuwar ‘yan kabilarsa su fada musu), hakan ya tilasta musu barinsa ba tare da suna so ba. Daga nan sai ya tafi zuwa wajen Zam-zam ya wanke jikinsa da raunukan da ya samu sakamakon bugun da mushirikai suka yi masa, yana mai farin ciki da wannan ‘yanci da haske na Musulunci da ya samu.

Bayan wannan bara’a da sanarwa, sai Abu Zar ya tafi wajen Manzon Allah (s.a.w.a) don ci gaba da samun koyarwa da tarbiyya ta Musulunci.

Bayan nan ma dai Abu Zar ya sake komawa don sake jaddada imaninsa, lokacin da ya sake jaddada ‘kalmar shahada’, nan take suka sake fada masa da bugu da duka, har suka ji masa raunuka masu yawa sai dai duk da haka bai bar imaninsa ba, don kuwa shi mumini ya fi dutse tsayuwa kyam saboda babu abin da zai kawar da shi.

Abu zar ya ci gaba da rayuwa tare da Ma’aiki (s.a.w.a) bayan imaninsa har lokacin hijira, inda bayan komawarsa Madina ya ci gaba da rayuwa a masallacin Ma’aiki (s.a.w.a) tare da sauran Sahabbai marasa abin hannu da aka fi sani da ‘Ashab al-Sufa’.

Abu zar al-Giffari ya halarci wasu yakukuwa tare da Ma’aiki (s.a.w.a), sannan kuma ya halifanci Ma’aiki a garin Madina lokacin fitarwa wasu yakukuwa.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Sahabin Manzo, Abu Zar al-Giffari (R.A)”