Sadaukar da Kai

Daga Sheikh mujtaba S Adam
Wata rana Kilina ta ce da Fensiri: Ya kake abokina?
Sai Fensiri ya amsa cikin fushi ya ce: Ni ba abokinki ba ne, na tsane ki. Sai ta amsa cikin cikin mamaki ta ce: Saboda me? Sai ya ce: Saboda kina goge rubutun da na yi.
Sai ta ce: Ai kuskure kawai nake gogewa. Sai ya ce: To me ya shafe ki? Sai ta ce: Saboda aikina shi ne gogewa. Sai ya ce: Wannan ai ba aiki ba ne. Sai ta ce: Aikina yana da amfani kamar yadda naka yake amfani.
Sai ya ce: Ka ji karya, ai wanda yake rubutawa ya fi wanda yake gogewa amfani. Sai ta ce: Ai goge kuskure daidai yake da rubuta abin da yake daidai.
Sai Fensiri ya dan yi shiru, sannan ya fada cikin fushi: Amma na ga kullum sai kankancewa kike yi. Sai ta amsa da cewa: Saboda kullum ina saukar da wani sashe nawa wajen goge kurakurai.
Sai Fensiri ya ce cikin murya kasa-kasa: Ni ma dai ina ji a jikina kullum ina raguwa. Sai Ta ce da shi, tana mai karfafa masa guiwa da cewa: Ba za mu iya amfanar wasu ba sai mun sadaukar da kawukanmu saboda su.
Sai Kilina ta dubi Fensiri cikin sanyin murya ta ce da shi: Har yanzu ba ka son ganina? Sai ya yi murmushi ya ce: Ta yaya zan tsane ki kuma, alhali sadaukarwa ta hada mu?!
Ka sani cewa: Kullum ka wayi gari kwanakin rayuwarka suna karewa, idan har ba ka iya zama Fensiri wajen sanya farin cikin a zukatan bayin Allah ba, to ka zama tamkar Kilina mai taushi wajen shafe musu bakin cikinsu da damuwarsu, imam Ali (a.s) yana cewa: Mutane iri biyu ne: Ko dai dan uwanka a addini, ko kuma dan uwanka a halitta.