May 29, 2023

Sabon Shugaban Nageriya bola Ahmed Tinubu Ya Fara Naɗa Mukamin Farko Bayan Rantsar Dashi

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Dele Alake a matsayin mai magana da yawunsa, sa’o’i kaɗan bayan rantsar da shi a yau Litinin.

Alake ya dade tare da Tinubu, in da har ta rike mukamin kwamishinan yada labarai da dabaru a ƙarƙashin Tinubu da ga 1999 zuwa 2007 a lokacin ya na gwamnan jihar Legas.

Haka kuma shugaban ya nada Ambasada Kunle Adeleke a matsayin zagin shugaban ƙasa.

Ya kuma naɗa shugaban matasan APC na kasa, Olusegun Dada a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yaɗa labarai na zamani.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Sabon Shugaban Nageriya bola Ahmed Tinubu Ya Fara Naɗa Mukamin Farko Bayan Rantsar Dashi”