June 5, 2023

Sabon jirgin saman Najeriya ya yi batan dabo.

 

Rahotannin dake fitowa daga Najeriya sun ce sabon jirgin ‘Nigeria Air’ da tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya gabatar wa jama’a kafin karewar wa’adin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi batar dabo, domin kuwa an neme shi an rasa.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar tace, yanzu haka mutane na ta cece-kuce dangane da inda jirgin ya shiga da kuma lokacin da ake saran ya fara aikin dibar jama’a, tare da neman shafinsa na intanet da zai baiwa jama’a damar sayen tikiti kai tsaye.

Jaridar tace binciken da ta gudanar ya nuna cewar tuni jirgin ya koma cikin tawagar jiragen ‘Ethiopian Airlines’ inda aka dauko shi domin ci gaba da gudanar da zirga zirgar da ya saba yi.

Binciken da jaridar tayi a ranar 1 ga watan Yuni, yace an ga jirgin kirar Boeing 737-860 yana zirga zirga tsakanin biranen Addis Ababa da Mogadishu kamar yadda na’urar zirga zirgar jiragen saman da ake amfani da shi ya nuna.

Rahotan binciken yace an kwashe kwanaki 4 ana sauya fasalin jirgin domin mayar da shi cikin jerin jiragen Habasha bayan sauya fentin da aka masa da kuma bikin nuna shi a birnin Abuja.

Bayanai daga Najeriya sun ce tsohon ministan sufuri Hadi Sirika yayi kokarin amfani da karfin mulki wajen tilasta hukumomin dake kula da sufurin jiragen sama a Najeriya su amince da jirgin da kuma bashi lasisin gudanar da aiki ba tare da bin ka’ida ba, kamar yadda babban daraktan hukumar kula da sufurin jiragen sama kaftin O.O. Lawani yayi zargi, a wata wasika da ya rubuta.

Jaridar tayi kokari domin jin ta bakin ma’aikatar sufurin jiragen saman Najeriya dangane da makomar jirgin ‘Nigeria Air’, amma shugaban sashen hulda da jama’a na ma’aikatar Odatayo Oluseyi yaki cewa uffan dangane da lamarin, yayin da majalisar wakilai ta gayyaci babban sakataren ma’aikatar sufurin jiragen sama domin yi mata bayani akan halin da ake ciki.

Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun ce babu wani jami’in hukumomin Najeriya dake magana akan makomar wannan jirgi, kuma duk kokarin da RFI Hausa tayi na magana da tsohon ministan sufurin Najeriya Hadi Sirika domin karin haske akan lamarin, abin yaci tura.

RFI HAUSA 5/6/2023 ✍️

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sabon jirgin saman Najeriya ya yi batan dabo.”