Sabbin Dokokin hada-hadan kudade a Nijeriya.

Babban bankin Najeriya CBN ya fitar da sababbin dokoki na hada-hadar kuɗaɗe a bankunan ƙasar.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, CBN ya taƙaita yawan tsaban kuɗade da ƴan ƙasar za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki.
Sanarwan na zuwa ne mako biyu bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun naira da aka sabunta.
Sabbin Dokokin sune kamar ha -:
1. Yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.
Idan mutum na son cire kuɗin da ya fi wannan adadi yawa to sai an caje shi kashi biyar cikin 100 ga mutum da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da zai cire.
2. Duk wanda ya je banki cire kudin da suka haura naira 50,000 da caki na banki da wani ya rubuta masa, to ba za a ba shi kudin ba. Yayin da dokar cire kuɗin da suka kai naira miliyan 10 ta amfani da caki a tsakanin bankuna daban-daban tana nan a yadda take.
3. Yawan kudin da mutum zai iya cirewa ta hanyar amfani da na’urar cire kudi ta ATM a sati kuwa shi ne naira 100,000, wato yawan abin da za a cire a ranar naira 20,000 ne kacal.
4. Takardun kudin naira 200 kawai bankuna za su dinga lodawa a cikin na’urar ATM.
5. Idan a wajen masu amfani da na’urar POS ne kuwa, naira 20,000 ce yawan kudin da mutum zai iya cirewa.
6. A yanayin da ake da tsananin buƙata kuwa da ba zai wuce sau ɗaya a wata ba, inda ake buƙatar cire kuɗin da yawansu ya fi wanda aka ƙayyade don wani dalili mai ƙarfi, to abin da za a bari mutum ya cire ba zai haura naira miliyan biyar ba, idan kuma kamfani ne to ba zai haura naira miliyan 10 ba.
Sannan a hakan ma sai an caji kashi biyar cikin 100 na yawan kudin ga mutum, da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da za a cire.
Ko wannan Sabbin Dokokin zasu zamo cikas ma Yan Nijeriya wajen kasuwan cin su ?