November 15, 2022

Rundunar sojojin Najeriya ta wallafa sunayen wasu mutane 19, wadanda ta ce tana nema ruwa a jallo

Rundunar sojojin Najeriya ta wallafa sunayen wasu mutane 19, wadanda ta ce tana nema ruwa a jallo, inda rundunar ta ce za a baiwa duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama kowane daya daga cikinsu, tukuicin Naira miliyan 5 kimanin dalar Amurka 11,300.
Cikin takarda mai kunshe da sunaye da hotunan mutanen 19, wadda rundunar sojin kasar ta fitar a jiya Litinin, an bayyana cewa, ana zargin su ne da aikata ta’addanci, sun kuma dade suna addabar al’ummun jihohin Katsina, da Sokoto da Zamfara.
Najeriya na fuskantar tarin kalubalen tsaro, kama daga ayyukan masu tsattsauran ra’ayin addini a arewa maso gabashin kasar, zuwa ’yan awaren Biafra a kudu maso gabashin kasar, da ma ’yan fashin daji da masu garkuwa da mutane a wasu sassan kasar.

©cri(Saminu Alhassan)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Rundunar sojojin Najeriya ta wallafa sunayen wasu mutane 19, wadanda ta ce tana nema ruwa a jallo”