February 10, 2023

Rundunar sojan sama na Iran, sun sake nunawa duniya wani barikinsu na karkashin kasa.

B abban Hafsan Hafsoshin rundunar sojan Iran, Major General Mohammad Hossein Baqeri tare da babban kwamandar rundunar sojan kasa na Jumhuriyar musulunci ta Iran Janaral Abdolrahim Mousavi ne suka kasance babban baki a wajen a yayin bude wannan babban barikin mai suna Oghab-44 (Eagle-44).

Barikin yana da wajen sauka da tashin jiragen sama, snnan yana iya daukar jiragen yaki da dama sannan yana dauke da mabuyar jiragen sama da kayan aikinsu na soja. Sannan barikin na dauke da wajen adana bayanai, bada umarni da kuma wajen gyaran jiragen da kuma yi musu sabis.

Barikin Oghab-44 na daya daga cikin barikokin karkashin kasa da yawa wanda sojojin Iran suka mallaka, wanda ana iya cewar kusan suna neman fin barikokinsu na sarari yawa. Galibin wadannan barikokin ana ginasu ne kusa da manyan tsaunuka da duwatsu domin nesantasu daga mazaunun jama’a, domin kuma su dace da zallar ayyukan soja.

Rahoto ya nuna cewar a wannan barikin ne ake ajiye manyan makaman mizayil irinsu Yasin, Qaem da Asef, wadanda jirage marasa matuka ke iya yin dakonsu a lokacin da bukatar hakan ta taso.
A kwanakin baya ma wannan rundunar sojan saman ta nunawa duniya wani barikin nata mai na jiragen sama marasa matuka zalla “Drone Base 313” wanda hakan ya kada hantar abokan gaba sosai.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Rundunar sojan sama na Iran, sun sake nunawa duniya wani barikinsu na karkashin kasa.”