April 7, 2024

Runduna ta 98 ​​tare da dakarunta uku sun fice a daren jiya daga Khan Younis

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto kakakin hukumar ta IOF cewa  dukkan sojojin kasa sun janye daga zirin Gaza in banda birged daya.

A cewar kafar yada labaran Isra’ila, runduna ta 98 ​​tare da dakarunta uku sun fice a daren jiya daga Khan Younis bayan shafe watanni hudu ana gwabza fada.

A halin yanzu dai rundunar Nahal Brigade ita ce daya tilo daga cikin sojojin da suka mamaye Gaza, domin ita ce ke da alhakin tabbatar da hanyar “Netzarim” don hana Gazan komawa Arewa.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Runduna ta 98 ​​tare da dakarunta uku sun fice a daren jiya daga Khan Younis”