September 2, 2021

Ronaldo ya karya tarihin Ali Daei na Iran a cin ƙwallo

Baba Abdulƙadir
Cristiano Ronaldo ya karya tarihin da Ali Daei dan kasar Iran ya kafa na tsahon shekaru 15 a duniya bayan ya ci wa kasar ta Portugal kwallo ta 110.
Dan wasan mai shekaru 36 ya yi daidai da tarihin Daei a gasar cin kofin Turai a wannan bazarar kuma ya ci kwallaye biyu a ragar Jamhuriyar Ireland a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya a daren Laraba da ta gabata,
Tun bayan dawowar Ronaldo Manchester United dan wasan ya shiga filin wasan Estadio Algarve da karfinsa,
Ronaldo, ya ci takalmin zinare daga gasar cin kofin Turai tare da kwallaye shida.
Dan wasan kasar Ali Daei ya ci wa Iran kwallaye 109 tun a tsakanin 1993 zuwa 2006.
Kwallon farko da Ronaldo ya ci a kasa ita ce kwallon da yaci a gasar Euro 2004 akan kasar Girka, kafin ya ci kwallon farko a wasan kusa da na karshe da Netherlands.
Da wannan sakamakon Portugal ce ta farko da maki 10, bayan wasa hutu da ta buga da tazarar maki uku tsakaninta da ta biyu Sabiya.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Ronaldo ya karya tarihin Ali Daei na Iran a cin ƙwallo”